Author: Muhammad Mubarak Bala SHARE ON FACEBOOK SEND VIA EMAIL Mazaunan Ojoro sun cafke wani dan yankan-kai a kusa da tashar Obadeyi, da ke kan hanyar Lagos zuwa Abeokuta Labari da dumi-dumi: An cafki wani dan yankan-kai a kan hanyar Lagos-Abekuta An ce an kama shi ne da aka jiyo ihun wata mata daga karkashin gadar dake kan hanyar, wacce ake zaton ’yan yankan-kai ne suka kama ta. ’Yan sandan da suke wajen sun kasa wanzar da zaman lafiya a yankin don mazaunan wajen sun kulla aniyar kashe mutumin.Labari da dumi-dumi: An cafki wani dan yankan-kai a kan hanyar Lagos-Abekuta Duba wannan: Mayakan Boko Haram sun kashe masunta 34 a jihar Borno Wani daga cikin mazaunan, Adesola John, yace, “An fara jiyo ihun wata mata ce sai aka fara bin dajin dake karkashin gadar dake kan hanyar, inda a nan aka ga mutumin da aka cafka. Ba’a ga matar dake ihu ba amma har yanzu ana nan ana ta binciken wajen. Wani ma da ya ki yadda a baiyana sunansa yace zai yi wuya ace matar ce kadai da aka boye a dajin. Dan rahotonmu da ke wajen yace har a halin yanzu ana nan ana bincike a dajin. Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Advertisements