Author: Abdulazeez Abdul UPDATED:  SHARE ON FACEBOOK SEND VIA EMAIL – Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya caccaki bankuna Najeriya cewa suna ba ‘yan fashi da biro mafaka – Magu ya ce bankuna na kokarin ganin an cire NFIU a karkashin EFCC – Magu ya zargi bankuna na so amfani da wani tsohon babban daraktan banki a matsayin shugaban NFIU domin ya kare su Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu ya zargi bankuna Najeriya a kan samar da yanayi ga ‘yan fashi da biro, ya ce, abin lura a nan shine bankuna na yin duk abin da zai yiwu don tabbatar da cewa an kawar da sashen leken asirin kudi na kasa wato Nigeria Financial Intelligence Unit, NFIU daga hukumar. Shugaban EFCC ya zargi bankuna Najeriya da taimkawa barayin gwamnatiMagu ya ce: “Ban yarda da bankuna kasar nan ba. Suna samar wa barayin gwamnati wani yanayi ta yadda za su iya awon gaba da dukiyar al’ummar kasar, abin da ya sa suke kokarin ganin an cire NFIU daga gare mu”. Magu ya ci gaba da cewa bankuna na so su yi amfani da wani tsohon babban daraktan banki a matsayin shugaban NFIU domin su ji karensu ba babbaka. Ibrahim Magu tare da tawagar lamuni na duniya, IMF

Advertisements