Author: Muhammad Auwal UPDATED:ON FACEBOOK SEND VIA EMAIL – Jarumin Kannywood Ali Nuhu yace zai daina rawa da waka – Sai dai shahararren dan wasan Hausan bai bayyana yaushe ne ba Shahararren dan wasan Kwaikwayo na Kannywood Ali Nuhu wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood ya bayyana ma BBC Hausa cewa ya kusa daina rawa da waka, amma fa sai idan lokaci yayi. Sarki Ali yace sau dayawa ya kan yi rawa da waka ne kadai idan hakan ya zama dole, musamman idan Fim din na bukatar ayi hakan. KU KARANTA: Zan daina yin rawa da waka a Fim, amma….. – Inji Ali Nuhu (KARANTA)Kwaya ce: Ýan mata da matan Aure sun koma harkar shan ƙwaya da kayan maye – Inji NDLEA Sarki Ali ya kara shaida ma majiyar NAIJ.com cewar idan da za’a kwatan ta irin rawar da yake yi a baya, za’a gane cewa ya rage sosai. Ali Nuhu Sai dai jarumin Fim din Hausan, wanda a yanzu shekarunsa 44 bai bayyana yaushe ne ranar da zai daina yin rawa ba. A wani hannun kuma a kwanan nan ne Ali Nuhu ya fitar da sabon Fim dinsa Mansoor, wanda masana suke ganin ya kawo sabon salo a Kannywood.

Advertisements