Author: Aisha Musa UPDATED:  Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) na shirin kama wasu ‘yan majalisa – Yan majalisan sun kasance sanatoci da aka zarga da aikata laifuka daban-daban a matsayin tsofaffin gwamnoni a jihohin su – Har ila yau suma ‘yan majalisa suna shirin kafa wani kudiri da zai umurci sanatoci da karda su amsa gayyatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) na shirin kai farmaki ga wasu sanatoci masu ci a majalisar dokoki, Daily Times ta ruwaito. Shawarar hukumar da yin wannan kamun ya biyo bayan zargin cewa wasu sanatoci na shirin kafa wata kudiri da zai hana abokan aikinsu da aka zarga da aikata laifuka daban-daban kin amsa gayyatar hukumar EFCC har sai an tsige shugaban hukumar Ibrahim Magu. NAIJ.com ta tattaro cewa majalisar dattawa na shiri don yin maslaha da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kan zarge-zarge daban-daban da ake yi a kan wasu sanatoci wadanda suka kasance tsofaffin gwamnoni. An tattaro cewa hukumomin yaki da cin hanci da rasahwa na ci gaba da samun wasikun korafe-korafe a kan wadannan sanatoci masu ci. KU KARANTA KUMA: Fr. Mbaka ya saki bam a kan lafiyar Buhari, ya ce ya ji kuka daga Aso rock Wata majiya daga majalisar dattawan ta ce wasu daga cikin sanatocin da abun ya shafa sun hada da tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio; tsohon gwamnan jihar Plateau, Joshua Dariye da Jonah Jang, tsohon gwamnan jihar Ebonyi Sam Egwu, tsohon gwamnan jihar Abia Theodore Orji da kuma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki. Majiyar ta kuma ce majalisar dattawa na shirin mika wani kudiri da zai umurci ‘yan Najeriya da ake bincike a yanzu da karda su amsa gayyatar hukumar har sai an tsige Magu. A baya NAIJ.com ta rahoto cewa ‘yan majalisa sunyi barazanar sanya kafar wando daya da sashin zartarwa idan har Magu ya ci gaba da kasancewa shugaban hukumar EFCC.

Advertisements