Author: Aisha Musa UPDATED: ON FACEBOOK SEND VIA EMAIL – Mista Oladipupo Adebutu ya tsallake rijiya da baya – Dan majalisan ya tsallake rijiya da baya ne a Ota, karamar hukumar Ado-Odo/Ota dake jihar Ogun a daren ranar Laraba Dan majalisar cdake wakiltan mazabar Ikene/Shagamu/Remo North, Mista Oladipupo Adebutu ya tsallake rijiya da baya a Ota, karamar hukumar Ado-Odo/Ota dake jihar Ogun a daren ranar Laraba. A cewar rahotanni, wasu da ake zargin yan iskan siyasa ne sun bude wuta ga ayarin motocin sa da misalin karfe 7:00 na yamma inda suka kashe daya daga cikin magoya bayansa a yankin Oke-Ide na garin. An rahoto cewa dan majalisar na a hanyarsa ta dawowa daga wani taro na jam’iyyar PDP a Aiyetoro, hedkwatar karamar hukumar Yewa North. KU KARANTA KUMA: EFCC tayi yunkuri a kan ‘yan majalisa, tana yunkurin kama wasu Sanatoci An rahoto cewa ya yada zango ne a Ota don kai wani ziyara ga wasu mambobin jam’iyyar da aka kama lokacin da aka kai masa hari. A cewar idon shaida, an harbe wani dan fadar dan majalisar da ba a bayyana sunansa ba, sannan kuma yam utu a take a gurin. 

Advertisements