Hotuna sun billon a wani karamin yaro wanda aka ce malamin islamiyar su ne ya daura masa mari a jihar Kaduna.

NAIJ.com ta gano cewa wata mai amfani da shafin Facebook Aishat Alubankudi ta yada hotunan wani dalibi a jihar Kaduna wanda aka rahoto cewa malamin Islamiyyar su mai suna Mallam Sufi ya daura masa mari. Ta yi kira ga wgwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai da ya taimaka ya ceci yaron.

A cewar ta: “Gwamna Mallam Nasir El-Rufai dan Allah ayi bincike. Wannan rahoto da ba’a tabbatar ba! An tura wannan yaron makarantar Islamiyya a Zaria daga kauyen Boko dake jihar Zamfara.

Kalli yadda wani malamin musulunci ya daure dalibinsa da mari (HOTUNA)

Kalli yadda wani malamin musulunci ya daure dalibinsa da mari

“Malamin sa ya daure sa da mari sannan kuma ya tura sa yin bara na abincin da zai ci. Sunan Mallamin Sufi, a yankin Rimin Tsiwa dake birnin Zariya jihar Kaduna. Makaranatar Islamiyyar na jikin gidan Alhaji Sani Rimin Tsiwa.

Advertisements