– Fasto yace tauraron Fani Kayode ya kusan dusashewa

– Kayode tsohon minista ne a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo

Wani fasto dan Najeriya amma mazaunin kasar Amurka, Fasto Moshood Ifayemiwo ya hango mutuwar wani dan adawan shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma tsohon minista, Fani Kayode.

Faston yace nan bada dadewa ba tauraruwar Kayode zata dusashe, kuma Kayoden ka iya mutuwa, kamar yadda Faston yace ya gano daga wasu karance karance da yayi a cikin littafin Bible.

NAIJ.com ta ruwaito Fasto Moshood yana fadin “Ban taba haduwa da Fani Kayode ba, amma na hangi halin da zai shiga a nan gaba, sai dai abin da na gani shine zai iya mutuwa nan bada dadewa ba, idan bai fara addu’a da kuma canza halayyarsa ba.” Inji Faston.

Fasto yayi hasashen mutuwar Fani Kayode, kamar yadda shima yayi hasashen mutuwar Buhari

Fasto Moshood da Fani Kayode

Advertisements