Sabanin jita-jitan da ke yaduwa cewa shugaba Buhari yayi wafati a kasar Ingila, ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, yace mukaddashin shugaban kasa na magana da shi kulli yaumin.

Ya bayyana wannan ne a Legas a wata hira da gidan Talabijin Channels mai suna Siyasar yau.

Game da cewar Lai Mohammen, Buhari yayi matukar yarda da Osinbajo kuma yana biyayyansa sosai.

Yace: “ Mukaddashin shugaban kasa na tattaunawa da shugaban kasa saboda haka inada yakininc cewa shugaban kasan na da cikakkaen masaniya game da abubuwan da mukaddashin shugaban kasan keyi kuma akwai yarda tsakaninsu kuma ban tunanin wannan matsala ne.”

Akan zancen garambawul, Lai Mohammaed yace wannan ba wani abun da ya kamata mu mayar da hankalinmu kai bane a yanzu.

Yace: “Nayi bayani a wurare daban-daban cewa abin da ke gaban wannan gwamnati shine zaman lafiya.

Advertisements