– Femi Fani-Kayode ya ce kila shugaba Muhammadu Buhari ya mutu

– Ya kalubalanci fadar shugaban kasa da ta daina yawo da hankalin jama’a ta filo fili ta bayyana gaskiya a kan halin da yake ciki

– Ya kuma ce a kawo hujja da zai tabbatar da cewa yana nan da ransa bai mutu ba kamar yadda suke ikirari

Tsohon ministan kula da sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayose ya ce babu mamaki kila ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu.

Hakan na kunshe ne a cikin sabon labara da ya aika ma jaridar Daily Post a safiyar ranar Juma’a.

Ya ce kunbiya-kunbiya da fadar shugaban kasa keyi ya sa ‘yan Najeriya cikin rashin kwanciyar hankali sannan kuma yasa suka kalubalanci gwamnati da ta saki hotunan shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar IboKalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar Ibo

Advertisements