– Wani mutum Mathew, ya kashe matarsa Hanna, mai dauke da juna biyu

– Masoyan sun dade sun zaman daduro kafin mummunan lamarin ya auku

Wani mutumin jihar Benuwe mai suna Mathew ya hallaka matarsa, abar kaunarsa, uwar yayansa uku, mai suna Hannah saboda wani abu da bai kai ya kawo ba, ko a ce, abinda bai taka kara ya karya ba.

Sudai wadannan matasa sun dade suna tare, amma a ranar da lamarin ya auku, Hannah wanda take dauke da ciki wata 8 ta ci duka a hannun Mathew a gidansu dake Abuja, sakamakon kin wanke masa kayansa daya bata ta wanke.

KU KARANTA: Watan Ramadana: Kwankwaso yayi rabon shinkafa

NAIJ.com ta gano dalilin daya hana Hannah wanke kayan Mathew kuwa shine, a ranar ta wuni a asibiti inda taje awo, ko da ta dawo, yamma yayi, don haka sai ta dage yin wanke sai washe gari. Da gogan naka ya dawo sai ya dinga fada, ita kuwa tana bashi hakuri.

Advertisements