Author: Muhammad Auwal UPDATED:  ON FACEBOOK SEND VIA EMAIL – Ministan harkokin matasa da Wasanni Solomon Dalung, ya soki lamirin gayyatarsa Musulunci da Pantami yayi – Dalung yace ya saurari ra’ayoyin jama’a da dama dangane da ziyarar ta sa Ministan harkokin matasa da Wasanni Solomon Dalung, ya soki lamirin hanyar da Sheikh Isa Ali Pantami ya bi wajen kiran sa da ya shiga addinin Musulunci, kamar yadda ya sanar a shafinsa na Facebook. A makon data gabata ne dai NAIJ.com ta ruwaito muku ministan ya kai ziyara a Masallacin Annur dake Abuja inda Sheikh Pantami Pantami ke gabatar da Tafsir cikin watan azumi. KU KARANTA: Shiriya daga Allah: Sarauniyar kyau ta Musulunta Dalung yace ya saurari ra’ayoyin jama’a da dama dangane da ziyarar tasa, Ban ji daɗin yadda Pantami yayi min tayin shiga Musulunci ba – Inji Solomon Dalungamma yace a gaskiya Shehin malamin ya tozarta shi ta yadda ya gayyace ya shiga musulunci. Inda yace: “Tayin da Pantami yayi min bada zuciya daya yayi shi ba, kuma ba akan tsarin Musulunci bane, da fari dai ba shi ya gayyace ni Tafseer din ba, da kai na naje. Pantami tare da Solomon Dalung “Na yi mamakin yadda Pantami ya ki yin koyi da Annabi SAW, wanda da ya karbi bakoncin tawagar Kiristoci daga birnin Sinai, kuma ya karbe su hannu biyu biyu ba tare da yayi musu tallar Musulunci ba, asali ma kyale su yayi sukayi bautansu a masallacin.” Dalung ya cigaba da fadin cewa kimanin shekaru biyar kenan ya na zuwa tafsir a masallatai daban-daban, domin karfafa dangantaka tsakanin addinin Kirista dana Musulunci, kuma ba’a taba yi masa haka ba, “Pantami yayi amfani da damar ne don kawai ya bata min suna, Inda a ce da gaske yake, me ya sa tun can baya bai taba yi min kiran ba, sai da na ziyarce shi? Ko kuma ya aiko mini a rubuce ba? Ina mu’amala da manyan Musulmai da dama kamar su Sheikh Lemu, Sheikh Dahiru Bauchi, Sarkin Musulmai, Sheikh Yahaya Jingir, Sheikh Khalid, Maitama Sule, Sani Zangon Daura, Ango Abdullahi,da sauransu, kuma dangantaka nay a kara min sanin addinin Musulunci.” Inji Dalung Daga karshe minista Dalung ya shawarci Musulmai da Kirista da su zauna lafiya da juna, sa’annan su kawar da kai daga dukkanin masu kulla rikici a tsakaninsu, kuma yace wannan lamari ya karfafa masa kwarin gwiwar cigaba da kokarin samar da fahimtar juna tsakanin addinan biyu.Ban ji daɗin yadda Pantami yayi min tayin shiga Musulunci ba – Inji Solomon Dalung

Advertisements