Shugabannin PDP zasu kai ma Buhari ziyara

Shugaban kungiyar amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Walid Jubril yace shugabannin jam’iyyar na shirin ziyara da juyayi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a birnin Landan.

Shugabannin PDP zasu kai ma Buhari ziyara

Jubril, wanda ya karyata cewan jam’iyyar ta taimaka gurin yada jita-jitan mutuwar shugaban kasa, ya bayyana cewa PDP na ta addu’a da dukka karfinta domin shugaban kasa Buhari ya dawo gida Najeriya cikin lafiya.

KU KARANTA KUMA: Atiku yayi kira ga sake fasalin al’amuran Najeriya

“Muna fatan ya samu lafiya sannan ya dawo ya ci gaba da shugabancinsa na Najeriya.

“Idan za’a bamu dma, shugabannin jam’iyyar PDP zasu je birnin Landan don yi mai fatan alkhairi da kuma taya yan iyalan sa alhini,” cewar sa a Kaduna.

Shugaban kungiyar na amintattu ya kuma yi magana a kan rikicin dake cikin jam’iyyar “jam’iyyar PDP bazata taba mutuwa ba.”

A cewar sa, jam’iyyar na kokari don ganin ta kawo karshen rikicin da take fuskanta.

“Da izinin Allah zamu fito a tsaftace kuma jam’iyyar PDP bazata taba mutuwa ba, zata shi gaba a matsayin jam’iyya mai karfi.”

Advertisements