Dalilin da ya sa na gina masallaci da coci wuri daya – Obasanjo

 

Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya gina coci da masallaci a wuri guda shine domin nuna anfanin hadin kai a tsakanin addinan biyu.

Dalilin da ya sa na gina masallaci da coci wuri daya - Obasanjo

Dalilin da ya sa na gina masallaci da coci wuri daya – Obasanjo

Tsohon shugaban yayi wannan jawabin ne a wata fira da akayi da shi a cikin shirin gidan Reduon Kaduna na Liberty Radio inda ya kara bayyana wa mutane muhimmancin zama lafiya tsakanin mabiya addinan biyu.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kira tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga kasar Ingila domin tayi shi murnan zagayowar ranar haihuwarsa yau.

An gudanar da bukin zagayowar ranar haihuwar Obasanjo yau a garin Abeokuta da kaddamar wata sabuwar dakin karatu da ya gina.

Buhari ya yabi Obasanjo kan irin shugabanci nagari da yayi musu a lokacin da suke aiki soji.

Bayan haka Buhari ya kira gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

Buhari yayi masa fatan alkhairi sannan ya ce masa lallai yana samun sauki kuma ya kusa dawo wa kasa Najeriya domin ci gaba da aiki.

Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo bai yi kasa kasa ba wajen yaba ma Buhari da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya.

Advertisements