– Shugaba Muhammad Buhari ya bada umarnin dawo da takobin Egbesu mai tsoho tarihi wanda sojoji suka kwace a wani sumame da suka kai yankin su na neman shugaban tsagerun mai suna Tampolo

-Umarnin na shugaban tare da ziyarar da mukaddshinsa Osinbanjo ya kai a yankin wani bangare ne na neman hanyoyin da gwamnatinsa ke bi don dawo da zaman lafiya a Niger-Delta

Hatsaniyar Niger Delta: Buhari ya bada umarnin a dawo da takobin Egbesu mai tsohon tarihi

Hatsaniyar Niger Delta: Buhari ya bada umarnin a dawo da takobin Egbesu mai tsohon tarihi

A shekarar da ta wuce 2016 ne, sojojin Najeriya su ka kwace wani takobin gwal na masauratar Gbaramatu a karamar hukumar Warri ta Kudu cikin jihar Delta.

Shugaba Buhari ya ba da umarnin da a nemo takobin da ita ce alamar masarautar Egbesu, a kuma dawo da ita ba tare da jinkiri ba.

Ci gaban na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ke kara damara wajen hakurkurtar da yankin na Niger Delta da ke fama da tashe-tashen hankula don inganta fitar da mai daga kasar

An rawaito cewa, sojojin runduna ta 4 ne daga garin Benin suka kwace takobin da a ke bayyanawa a matsayin tambarin karfin ikon masarautar Gbaramtu a watan Mayun sekarar 2016, a yayin da su ke neman tsohon jagoran masu tayar da kayar baya, Government Ekpomukpolo da a ke wa kirari da Tompolo a lokacin da lalata kayayyakin hakar mai ya yi kamari a yankin.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, baya ga dawo da takobin, fadar shugaban kasa ta amince ta fitar da kudi don gaggauta fara tafiyar da jami’ar Maritime, wacce ta gamu da tasgaro sanadiyyar rikice-rikicen yankin da kuma rashin kudi.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta fadawa Jaridar Vanguard cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin bincikowa da kuma dawo da takobin da ke zaman alamar fadar Egbesu zuwa masauratar Gbaramatu nan take.

Jami’in da ya nemi a boye sunansa , ya ce yunkurin na fadar shugaban kasa na dannar kirji ga yankin na Niger Delta ya zo daidai da shawarar da gwamnati ta yanke ta kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin da kuma kawo karshen lalata kayayyakin harkokin tattalin arziki da ke cutar da kasa.

Majiyar ta tabbatar da cewa a kokarin hakurkurtar da yankin na Niger Delta, shugaba Buhari ya tura mataimakinsa Yemi Osinbajo ya je ya hadu da manyan shugabannin Niger Delta duk da cewa ba ya nan.

Jami’in ya bayyana ziyarar da Osinbajo ke yi a yankin da ‘kamfe din diflomasiyya’ don kawo karshen rikice-rikicen yankin. Vanguard ta gano cewa duk dai a bangaren sulhun, fadar shugaban kasa ta yanke shawarar tsayar da amfani da karfi a kan ‘yan tawayen na Niger Delta don bada damar tattaunawa da kungiyoyin da su ka bayyana, kamar su Pan Niger Delta Elders Forum (PANDEF).

Jami’in ya ce:

“Shugaba Buhari ya umarci mataimakin shugaban kasa ya je ya duba ya kuma kawo cikakkun bayanai game da ziyarce-ziyarce zuwa duk jihohin da ke da man fetur ya tabbatar an duba bukatunsu ba tare banbancin jam’iyya ko kuma kowane irin banbanci ba.”

Idan za tuna, Cif Government Ekpemupolo ya yi barazanar daukar matakin gano takobin gwal din.

Tompolo, a wata budaddiyar wasika da ya rubutawa shugaba Muhammadu Buhari ya ce a wani hari da sojin Najeriya su ka kai kan al’ummarsa sun dauke masa tambarin iko na babban jagoran fadar Egbesu, Oporoza a masauratar Gbaramatu.

Vanguard ta rawaito cewa, tsohon dan tawayen na Niger Delta ya ce lamarin ya faru ne kimanin kwanaki 31 da su ka wuce lokacin da sojojin su ka afkawa Oporoza su na nemansa lokacin ba ya nan, a zargin da su ke masa na saka bom a kayan aikin danyen mai a yankin.

Tompolo, a wata wasika zuwa shugaban kasa ya bayyana burinsa na haduwa da shugaba Buhari. “Bangarena na labaru da dama da aka fada maka a kaina”

Ga ra’ayin jama’a kan lafiyar shugaba Buhari

Advertisements